Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya tafi kasar Equatorial Guinea a cewar Kakakinsa Ajuri Ngelale.
Wata sanarwa da Ngelale ya fitar ta ce Tinubu zai kwashe kwanaki uku yayin ziyarar don ganawa da Shugaba Teodoro Obiang Nguema Mbasogo.
“Da zarar ya isa, Shugaba Tinubu zai hadu da takwaran aikinsa na Equatorial Guinea, inda shugabannin biyu za su yi zama don cimma matsaya kan batutuwan mai, iskar gas da tsaro” Ngelale ya ce.
Sanarwar ta Ngelale ta kara da cewa, “Ministan harkokin wajen Najeriya, Ambassada Yusuf Tuggar da sauran mambobin majalisar zartarwarsa za su rattaba hannu kan yarjeniyoyi tare da duba wasu hanyoyi da kasashen biyu za su yaukaka dangatakarsu.”
Ziyarar ta Tinubu mai shekaru 72, na zuwa ne kasa da makonni biyu bayan zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi a kasar wacce ta fi yawan al’uma da karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka.
Najeriya ita ce kasar da ta fi yawan arzikin mai a nahiyar Afirka.
Equatorial Guinea tana matsayi na 10 a nahiyar Afirka cikin kasashen da suke da arzikin na man fetur a nahiyar a cewar kamfanin da ke kididdiga kan arzikin man fetur na Statista.
Dandalin Mu Tattauna