Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya jagoran taron babbar majalisar kasa karon farko tun hawansa kan karagar mulkin kasar, domin tattauna halin da kasa take ciki da zimmar samun kyakkyawar makona.
Taron ya gudana ne ‘yan kwanaki bayan zanga-zangar da ‘yan Najeriya suka gudanar, bisa korafin “rashin kyakkyawan shugabanci” wanda ya haddasa tsadar rayuwa, yunwa, fatara da rashin tsaro.
Akasarin ‘yan kasar na dora alhakin mawuyacin halin da ake ciki da wasu kudurorin gwamnatin Tinubu, da suka hada da ba da sanarwar janye tallafin man fetur a ranar farko da aka rantsar da shi ba tare da wani kwakkwaran shiri ko tanadi ba, janye tallafin wutar lantarki da sauransu.
Taron majalisar wadda ta kumshi tsofaffin shugabannin kasar da alkalan-alkalai da gwamnonin kasar, ya tattauna kan zanga-zangar da abubuwan da suka haddasa ta da kuma abubuwan da ita ma ta haddasa, musamman a yadda ta rikide zuwa bore a wasu yankuna.
A lokacin taron, shugaba Tinubu ya yi bayanin matakan da gwamnatinsa ke dauka wajen farfado da tattalin arzikin kasa, ta hanyar inganta aikin gona, ilimi, kasuwanci da masana’antu da kuma samar da aikin yi ga matasa.
Yayin da yake karin haske kan taron, Ministan ma’adinai na Najeriyar Dele Alike, ya ce majalisar ta nuna amincewarta da matakan na Tinubu.
Ministan ya kuma bayyana cewa majalisar ta amince cewar zanga-zangar da aka gudanar ta lumana amma ta rikide zuwa tarzoma a wasu yankuna, “ba abu ne mai alheri ga kasar tsarin dimokaradiyya ba.”
Shi ma jami’in yada labarai na fadar shugaban kasa Abdulaziz Abdulaziz, ya bayyana cewa sauye-sauyen da shugaban kasar ya fito da su, suna da manufar bunkasa tattalin arzikin kasa da ‘yan kasa, amma kuma dole ne sai an yi hakuri domin wasu ba za su yi wa ‘yan kasa dadi ba a halin yanzu.
Abdulaziz ya kara da cewa a wajen taron majalisar ta kasa ta bayyana amincewarta da kudurorin na shugaban kasa, inda ta karfafa masa gwiwar kara azama wajen kawo sauki kan halin matsin rayuwa da ‘yan kasar suke ciki.
Saurari cikakken rahoton Umar Faruk Musa.
Dandalin Mu Tattauna