"Wannan mawuyacin lokaci ne, to amma kawancen nan mai dinbin tarihi na Amurka da mutanen Koriya Ta Kudu masu karfin hali bai taba yin karfi ba irin wannan," a cewar Pence a birnin Seoul a yayin wata liyafar cin abinci da 'yan'uwan sojojin Amurka da ke Koriya Ta Kudu.
"Wannan takala ta safiyar yau dinnan da Koriya Ta Arewa ta yi, shi ne na baya-bayan nan na al'amuran da ke tunatar da mu irin hadarin da kowannenku ke fuskanta kulluyaumin a kokarin kare 'yancin mutanen Koriya Ta Kudu da kuma kare Amurka a wannan bangare na duniya," a cewar Pence .
Tunda farko a jiya Lahadi din sai da Mataimakin Shugaban kasa ya halarci addu'ar Majami'a na bukin Ista tare da sojojin.
A cewar kafar labarai ta Associtaed Press, manufar wannan ziyara ta farko da Pence ya kai a Koriya Ta Kudu ita ce ya bayyana ma Shugabannin Japan, Indonesiya da Australiya da Koriya Ta Arewa wani sabon mai suna "Matukar matsin lamba da kuma tattaunawa" da zummar kara matsa ma gwamnatin Koriya Ta Arewa.
Facebook Forum