A yau Asabar wata alkalin kotun gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin da ake yi na kaddamar da hukuncin kisa akan wasu mutane guda shida nan da kwanaki goma masu zuwa.
Da fari dai gwamnatin jiha ta yi shirin kaddamarwa da takwas daga cikin wadanda aka yankewa hukuncin su fiye da goma sha daya sati biyu kafin su sayi Midazolam, Midazolam dai Allura ce mai hadarin gaske wadda ake zaton ta lalace. Amma wani Alkalin ya bada damar a tsayar da Masu laifin guda biyu.
Wadanda aka yankewa hukuncin kinsan sun gabatar da karar a jihar, inda suka ce Midazolam zata sa su fuskantar matsananciyar azaba.
Mai shari’ar gwamnatin ta rayyar Kristine G. Baker da ke Little Rock ta bayyana cewa ta yanke wannan hukuncine saboda masu gabatar da hukuncin kinsan basu da makarin Allurar a hannu idan wani abu na bazata ya faru a yayin gudanar da hukuncin, wanda tace hakan na iya yiwuwa kamar yadda aka ga misalai a jihohin Alabama, da Arizona da Ohio da kuma Oklahoma a lokacin da akayi amfani da Allurar ta Midazolam.
Facebook Forum