Yayin da yake yiwa jama'ar jihar jawabi gwamnan jihar Ibrahim Dankwanbo ya gaya masu su kara hakuri da gwamnatinsa domin shekaru uku da suka wuce jihar na cikin jihohin da suka fi talauci a kasar. Ya ce yau kidigdiga da suka samu jihar da cikin jerin jihohi uku da suka fi samun habakar tattalin arziki. Ta bi bayan Legas da Kano ne kawai.
To sai dai wasu talakawa ta bakin Garba Tela talauci na nan a jihar Gombe. Ya ce suna da talaucin kudi fiye da yadda kowa yake tsammani. Ya ce wanda ya koshi baya jin yunwa. Gwamna yana ganin kudi a gabansa don haka ba zai san halin da talakawa ke ciki ba. A cewarsa talauci bai je koina ba a jihar. Mutane basu da kudin sayen komai. Idan kuma an ce babu talauci a Gombe tamkar an ci amanar talaka ne.
Masanin harkokin yau da kullum Malam Musa Isyaku ya ce an samu cigaba ajihar to amma har yanzu akwai rashin aikin yi. Ya ce duk da kokarin gwamnan wadanda ke kusa da shi su ne suke jawo masa bakin jini.
Abduwahab Mohammed nada rahoto.