Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 12 Sun Mutu a Hadarin Legas


Cunkoson Ababan Hawa a Jihar Legas
Cunkoson Ababan Hawa a Jihar Legas

Akalla mutane 12 aka tabbatar da mutuwarsu bayan wani hadarin mota da ya uku a cikin birnin Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Hadarin ya hada ne da wata motar bus kirar Toyota da ta taso daga jihar Jigawa da ke arewacin kasar da kuma wata babbar mota.

Lamarin ya faru ne a karshen makon nan inda da rahotanni suka nuna cewa direban bus din ya yi bacci ne, lamarin da ya sa ya tsallaka hanun da ba nasa ba kuma suka yi taho mu gama da wata motar trailer.

“Mutum tara ne suka mutu, daga baya kuma aka kawo gawarwaki uku.” Inji Gambo Ubba, wanda ya shaida abin da ya faru.”

Hadarin mota a Njeriya na daya daga cikin ababan da ke haifar da hasarar dumbin rayuka a kasar, ko saboda rashin kyawun hanya ko taya mara kyau ko kuma tukin ganganci.

Domin ji cikakken bayani dangane da wannan abin alhini, saurari rahoton wakilin Muryar Amurka, Babangida Jibril daga Legas:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG