Shaidu a yankin arewacin Najeriya sun ce tarzomar da ta biyo bayan zaben shugaban kasa ta haddasa munanan abubuwa a wasu wuraren, inda ake ganin konannun gawarwaki a kan tituna, da gidaje da wuraren ibadar da aka kona kurmus, da kuma asibitocin dake cike da mutanen da suka ji rauni.
Jiya talata, shugaba Goodluck Jonathan ya sake nanata kiran da a kawo karshen wannan tashin hankalin da ya samo asali daga nasarar da hukumar zabe ta ce ya samu. Ya yi kira ga dukkan shugabannin siyasa da na addini da su yi tur da wannan tashin hankali.
Har ila yau, shugaba Jonathan ya dakatar da ministansa na harkokin cikin gida, Kyaftin Emmanuel Eheanacho, amma bai bayyana dalilin yin hakan ba. Tarzoma ta barke a yankin arewacin Najeriya inda Musulmi suka fi yawa a ranar litinin, a bayan da aka samu labarin cewa Mr. Jonathan, wanda Kirista ne, ya kayar da tsohon shugaban gwamnatin mulkin soja, Muhammadu Buhari, a wannan zaben.
Jam’iyyar Janar Buhari tana kalubalantar sakamakon zaben, amma a jiya talata, janar din yayi Allah wadarai da wannan tashin hankali yana mai fadin cewa jam’iyyarsa ba ta goyon bayan irin wannan martani.
‘Yan kallon zabe sun ce im ban da dan abinda ba a rasa ba, an gudanar da zaben babu ha’inci, amma ‘yan hamayya a Najeriya sun ce an yi magudi.
Jami’an gwamnati da kungiyoyin agaji sun ki bayyana yawan mutanen da suka rasa rayukansu a saboda fargabar cewa yin hakan zai iya haddasa wata fitinar ta neman ramuwar gayya.
Kungiyar agaji ta Red Cross ta Najeriya ta ce mutane akalla dubu 16 sun rasa gidajensu, yayin da wasu kusan 400 suka ji rauni. Da dama daga cikinsu sun ji raunuka na harbin bindiga ko adda.
Shaidu suka ce an yi sabuwar tarzoma jiya talata a wasu sassan Jihar Kaduna. Sojoji masu yawa sun yi sintiri kan tituna a fadin arewacin Najeriya domin hana barkewar sabuwar fitina.
Babu daya daga cikin jam’iyyun hamayya na Najeriya da ta yarda ta sanya hannu a kan sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi, kuma jam’iyyar CPC ta Janar Buhari ta shigar da kara tana kalubalantar sakamakon.