Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jonathan Ya Sha Alwashin Gudanar Da Zabe Kamar Yadda Aka Saba Duk Ko Da Tashe-Tashen Hankula


Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan.
Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan.

Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan ya ce za a gudanar da kashi na karshe na zaben Nijeriya kamar yadda aka tsara, duk ko da tashe-tashen hankulan da su ka biyo bayan zaben shugaban kasar.

Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan ya ce za a gudanar da kashi na karshe na zaben Nijeriya kamar yadda aka tsara, duk ko da tashe-tashen hankulan da su ka biyo bayan zaben shugaban kasar.

Mr. Jonathan ya fadi a wani jawabin da aka yada a fadin kasar a yau Alhamis cewa ana samun kwanciyar hankali, don haka ya yi alkawarin cewa za gudanar da zaben gwamnonin kamar yadda aka tsara.

Masu lura da al’amura sun ce zaben na karshe, wanda zai zo ne bayan zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisa, na iya zama mafi muni.

Mr. Jonathan ya fadi yau Alhamis cewa tashe-tashen hankulan suna tunatar da jama’a irin abubuwan das u ka faru a 1960 zuwa sama wanda ya haifar day akin basasa na watanni 30

A halin da ake ciki kuma kungiyar Red Cross ta ce tashe-tashen hankulan da su ka biyo bayan zabe a arewacin Nijeriya, sun raunata mutane 410 suka kuma raba mutane 40,000 da muhallansu.

Da alamar tashe-tashen hankulan sun lafa zuwa jiya Laraba, bayan dad an takarar shugaban kasa da bai yi nasara ba, Muhammadu Buhari y ace zai kalubalanci sakamakon zaben, amman ya roki magoya bayansa su kai zuciya nesa.

Rahotanni sun ce mai yiwuwa wajen mutane 50 ne su ka mutu sanadiyyar rikicin, kodayake jami’an gwamnati da cibiyoyin agaji sun ki fadin adadin mutanen das u ka hallakan, gudun kar hakan ya iza ramuwar gayya.

XS
SM
MD
LG