Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ce Ranar Radiyo Ta Duniya da Majalisar Dikin Duniya Ta Kebe


Radiyo irin na yanzu
Radiyo irin na yanzu

Ita ranar ta radiyo ta duniya ta samo asali ne daga shawarar da hukumar ilimi, kimiya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato EUNESCO na ware kowace ranar 13 ga watan Fabrairu ta zama ranar karrama radiyo biyo bayan kafa radiyon MDD a irin wannan ranar a shekarar 1946.

Hanyar sadarwar radiyo ta zama kafa da bata da na biyu wajen saurin isar da sako zuwa sako sako da lungunan duniya musamman a kasashe masu tasowa inda ba'a faye samun wutar lantarki kodayaushe ba.

Ministan wasanni da matasa na Najeriya Solomon Dalung na cikin 'yan Najeriya dake sauraren labarun radiyo kullum.

Barrister Dalung yace radiyo ya taka rawa kwarai wajen taimakawa talakawa ta gane 'yancinsu. Wajen girka dimokradiya radiyo yayi taimako. Haka ma wajen kiwon lafiya da aika sakonni da sada zumunci tsakanin al'umma.

Ga kuma wani misali na sauraren radiyo da shugaba Buhari ya bayar a jajiberen zaben 2015. Yace a radiyon Muryar Amurka ya ji wani na cewa zai sayar da katin zabensa domin ya sayi buhunan masara ma gidansa su ci. Wasu mata ma sun ce zasu sayarda katunansu saboda talauci.

Shugaban kungiyar muryar talakawa Zaidu Bala Kofa Sabuwa na ganin cancantar shagali a wannan ranar saboda, injishi radiyo ya zama tamkar makaranta.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG