Shugaban hukumar zaben na ihar Alhaji Muhammad Abdu Joro ne ya bayyana sakamakon zaben ga manema labarai.
Karo na ukku ke nan da gwamnatin jihar ke gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar tun lokacin da gwamna Ibrahim Geidam ya kama madafin ikon jihar.
Amma sakamakon ya zo wa mutane da mamaki ganin cewa duk shugabannin kananan hukumomin 'ya'yan jam'iyyar APC ne, jam'iyyar dake mulkin jihar. Babu kuma wani abokin hamayya da ya kalubalancesu.
Alhaji Muhammad yace a gaskiya duk shugabannin kananan hukumomin da suka samu nasara 'yan APC ne. Dangane da ko babu wata jam'iyyar da ta tsaya takara sai shugaban hukumar yace akwai wani a Potiskum amma daga karshe sai yayi watsi da zaben yayi tafiyarsa. Kuma ya rubuta cewa shi ya janye daga takarar.
To saidai wani saurayi da ya tsaya neman kujerar kansila a karkashin jam'iyyar CDC a Damaturu yayi zargin cewa an yi masu magudi kuma basu amince da sakamakon ba. Yace gwamnati ta aika da jami'an tsaro a nasu yankin cikin garin Damaturu din inda suka kori wakilansu suka kuma dangwala hannu kan kuri'u dari bakwai ma kansu.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.