Tawagar Najeriya da ta halarci taron nazarin hanyoyin magance sauyin yanayi a Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa COP28 ta kumshi mutum 1, 411.
Tuni 'yan Najeriya su ka caccaki wannan gagarumar tawaga ta shugaba Bola Tinubu a taron, yayin da gwamnati ke cewa ta na fama da karancin kudi.
Duk da yake mutum 97, 000 daga kasashe 100 suka halarci taron, amma masu sharhi na cewa tawagar ta Najeriya ta wuce gona da iri, don tamkar wasu sun tafi don ganin gari ne kawai.
To sai dai mai taimakawa shugaba Tinubu kan sha'anin watsa labarai Temitope Ajayi, ya fitar da sanarwa mai cewa ba dukkan 'yan tawagar ne gwamnati ta dauki nauyinsu ba.
Ajayi ya ce akwai 'yan kasuwa, masu fafutukar kare muhalli, jami'an sassan gwamnati har ma da 'yan jarida 20 daga kafafen yada labarai daban-daban da su ka halarci taron.
Mai taimakawa shugaban kasar ya nuna cewa wasu daga cikin tawahgar su su ka dauki nayin kan su don amfana daga taron.
Duk da haka an fahimci Temitope bai yi bayani kan kimanin mutum 600 da ake cewa fadar Aso Rock ce ta dauki nauyin su don raka shugaba Tinubu taron ba.
Najeriya na daga cikin kasashen da kan tafi taruka a kasashen duniya da tawagar mutane masu yawa, inda wasu ba su wuce masu rike jaka ko farantawa manyan 'yan tawagar rai ba.
Dandalin Mu Tattauna