Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Kwai Abin Dubawa Ga Sabon Fefen Bidiyon Da Kungiyar Boko Haram Ta Fitar


Ibrahim Shekau shugaban kungiyar Boko Haram
Ibrahim Shekau shugaban kungiyar Boko Haram

A sabon fefen bidiyo da kungiyar Boko Haram, ta fitar shugaban kungiyar Abubakar Shekau yayi gargadin cewa zasu dagula lamarin babban zabe dake tafe.

Batun da masana harkar tsaro da zamantakewa ke ganin a kwai abin dubawa ga sabon fefen bidiyon da kungiyar ta fitar. Mallam Muhammad Abdulhamid, na cibiyar kawo sauyi dakuma cigaba wato CCD a takaice yace dole ayi karatun ta nutsu, ga barazanar da kungiyar keyi cikin kwanakin nan. Inda yace dama akwai abubuwan da ake lura da shi, dayake a yanzu a kwai illimin fasaha kamar na na’ura mai kwakwalwa, wanda akwai masana harshe da zasu iya kallon bakin mutum alokacin da yake magana a bidiyo domin tabbatar da lamarin gaskiyar cewa shin mutumin ne yake magana ko bashi bane, saboda za’a iya sarrafawa mai magana daban wanda yake jikin hoton bidiyon daban.

A bangaren masu kada kuri’a kan barazanar ta kungiyar Boko Haram, a inda wani dan Najeriya yace, fefen bidiyo bazai razana mu ba, kuma wannan zabe muna jiran Allah ya kawo ranar sa, zabe kan zamu fita zamuyi ba gudu ba ja da baya.

To sai dai kuma suma jam’iyyun dake shirin shiga zaben, sun fara maida martani ga irin wannan barazana dake fitowa a yanzu. Alhaji Hardo dake zama shugaban babbar jam’iyyar adawa ta APC a jihar taraba yace fa, su basu razana ba “Mu a shirye muke zamu fito zabe koda za’a jefa mana boma bomai ne kamar zuwan sama, zamu fito mu zabi wanda muke so.”

Wannan dai na zuwane a yayin da hedikwatar tsaro ke fitar da sanarwar nasarorin da dakarun soja ke samu a kan mayakan Boko Haram cikin kwanakin nan. Inda a bangare guda ‘ya ‘yan kungiyar ke zafafa munanen hare-haren da suke kaiwa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00

XS
SM
MD
LG