Yayin da yake bude taron babban sakataren kungiyar Kanal Musa Shehu mai ritaya ya tabo abubuwa da dama da kungiyar ta yi domin warware wasu matsaloli.Cikinsu har da batun matsalar tsaro, da rabuwar kawunan al'ummar arewa da tabarbarewar tattalin arziki da rigingimun addini da na kabilanci da halin da nahiyar take a siyasar Najeriya.
Dangane da batun rabuwar kawunan al'ummar arewa sakataran ya ce kabilu daban-daban da da can suna zama lafiya da junansu sai gashi yau ba jittuwa tsakaninsu.Ya ce kalubalen matsalolin rashin zaman lafiya da hadin kai da tashin tashina su ne suka dauki hankalin kungiyar a 'yan shekarun da suka gabata.
A cigaba da jawabinsa sakataran ya tabo irin kokarin da kungiyar ta yi na warware matsalolin da suka addabi arewacin Najeriya, musamman kokarin da kungiyar ta yi na shawo kan kungiyar Boko Haram. Ya ce kungiyar ta yi taro da jami'an gwamnatin tarayya da mai ba shugaban kasa shawara kan sha'anin tsaro duk a kokarinsu na dakile tashin tashinar nahiyar. Ya ce ACF ta damu matuka da rashin samun daidaitawa da kungiyar Ahalus Suna ko Boko Haram.
Bisa duka alamu harakar tsaro da tattalin arziki da inda arewa ta samu kanta a siyasance suna cikin abubuwan da kungiyar zata dauki dogon lokaci tana muhawara akai.
Nasiru Birnin Yero nada rahoto.