Wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya ya samu ya zagaya cikin birnin Abuja yau da shugabannin PDP ke yin taro a birnin domin samun amsar wadannan tambayoyi.
Malamm Abubakar Ibrahim Lere cewa ya yi PDP itace matsalar PDP domin tun can farko bata kafa kanta kan turbar gaskiya ba. Idan an zo zaben shugaban kasa muddin shugaban ya nuna cewa ga wanda shi ya keso a tsayar ya yi takara to ko an bi tafarkin rashin gaskiya. Ba za'a taba samun masalaha ba. Shi kuma Saminu Yelwa Yawuri cewa ya yi Bamanga Tukur shi ne umal uba isan matsalar PDP domin yana son shugaban kasa ya zarce a zabe mai zuwa lamarin da ya sabawa matsayin gwamnonin jam'iyyar. Ta dalilin haka har ma ya fada karara cewa tikiti kwaya daya za'a yi. Ba za'a yi zaben fitar da gwani ba domin a sharewa Goodluck Jonathan faggen zarcewa a zaben 2015.
Buhari Inusa Kumo na ganin cewa Bamanga Tukur ba shi ne matsalar ba. It kanta jam'iyyar ta san matsalarta. Ya ce ko an cire Bamanga Tukur aka maye gurbinsa da wanda bashi da ra'ayin gwamnoni sai na shugaban kasa to ba za'a samu sulhu ba. Ma'ana muddin aka sake dora dan amshin shattan shugaban kasa rigingimu ba zasu kare ba. Manufar da shugaban ya kawo itace ta jawo masu baraka. Inda Bamanga Tukur zai sake manufarsa za'a samu daidaituwa.
Sule Garko kamar Abubakar Ibrahim yace rashin adalcin jam'iyyar da rashin gaskiya da zalunci su ne suka jawo rudanin da jam'iyyar ta samu kanta ciki. Shi ko Aminu Maialayafo cewa ya yi shugaba Goodluck shi ya jawo rikicin. Inda zai yarda kowa ya tsaya zaben fidda gwani na takarar 2015 za'a samu zaman lafiya.
Ga karin bayani a rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.