Kungiyar mai suna Dandalin Fasaha Ta Arewa Maso Gabas ta bukaci ta gana da duk gwamnonin jihohin shida ta fada masu da su samo hanyar magance rashin zaman lafiya da samo ma matasa aikin yi da kawar da fatara da bada ingantacen ilimi domin su matasa su zama mutane na kwarai.
Shugaban kungiyar Dauda Mohammed Gombe ya ce makasudin na zuwa taro a Bauchi shi ne su sake nanata babbar matsalar da ta addabi yankinsu na rashin tsaro lamarin da ya sa harkokin kasuwancinsu da ilimi duk sun tabarbare wasu ma sun tsaya cak. Ya ce suna da jihohi shida ayankin kuma babu wata jiha da bata da matsala.
Borno da Yobe sun fi fadawa cikin halin kaka-ni-kayi sanadiyar aikin ta'adanci. Bauchi da Gombe suna da nasu matsalar kana matsalar kabilanci da addini ta addabi jihar Taraba.Ya ce duk wadannan ba wani abu bane ya jawosu illa yadda aka yi watsi da matasa tun can farko. Basu samun ilimi kikakke. Babu aikin yi kana ga rashin tsaro. Jihohin sun manta da matasa. Ba'a daukesu suna da mahimmanci ba.
Da aka ce yawancin matasan mukaman siyasa suke bida sai Dauda ya ce su ba mukaman siysa suka damesu ba. A'a suna bukatar a basu horo da ilimi. A koya masu sana'o'i da zasu taimakesu su kama gaban kansu ba tare da dogara kan wani ba.
Abdulwahab Mohammed nada karin bayani.