Mazauna Zungeru da aka kwace kauyukansu da gidajensu da gonakansu suna zargin gwamnatin tarayya da kasa cika alkawarinta na biyansu diya.
Ko a baya ma dai al'ummomin sun yi wani yunkuri na dakatar da aikin sabili da korafinsu.
Shugaban kungiyar neman hakin al'ummarsa yace an kwace filayen da suka gada daga kakanninsu an kuma danne masu hakinsu. Yace har yanzu ba'a biyasu diya ba kuma wadanda aka biyasu abun da aka basu bai taka kara ya karya ba.
Shugaban mutanen ya dora laifin akan sarkin Minna Mai Martaba Umar Faruk laifin. Shi ne ya nada kwamiti ya zakulo lauyoyi yayi yadda yake so da lamarin. Sun je wurin sarkin amma wai sai ya yi tayin alkawarin zashi Abuja amma babu abun da ya fito. Yanzu shekara biyu ke nan suna taro da sarkin amma babu nasara.
Duk kokarin jin ta bakin Sarkin Minna din ya cutura. Amma wakilin gwamnatin tarayya Garba Shehu yace a tsarin da suka yi da akwai adadin kudin da gwamnati zata ba duk wanda lamarin ya shafa. To saidai yanzu gwamnatin tarayyan tare da ta jiha suna nazarin irin karin da za'a yi. Amma ya roki mutanen suyi hakuri su bari a cigaba da aikin madatsar ruwan.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.