Iskar siyasar da ke kadawa ce ta sa hukumomin jahar Kaduna su ka mayar da hankulan su ga kyautatawa jama'ar su wutar lantarki, ko dai kawai ganewa suka yi cewa hasken wutar lantarki na cikin abubuwan da ke habaka tattalin arzikin kowace kasa a duniya? Ko ma meye dai dalili mazauna garin Kaduna na bayyana farin cikin su da yadda suke samun wutar lantarki a kan kari ba kamar a kwanakin baya ba.
Duk da dan wannan ci gaba da ya fara samuwa a Kaduna, da sauran rina a kaba, kuma akwai jan aiki a gaban mai gona, kafin illahirin duka gidajen kasar Najeriya su wadata da hasken wutar lantarki, saboda kamar yadda kowa ya sani bangare ne mai fama da koma bayan da ya haifar da durkushewar masana'antu masu yawa wadanda dole sai wutar lantarki za su iya tafiyar da ayyukan su.
Najeriya na cikin kasashen duniya da suka fi yin amfani da injunan janareta domin samar da hasken wutar lantarki a cikin gidaje da ma wuraren sana'o'in da dole sai da wutar za'a yi.
Wakilin Sashen Hausa a Kaduna Nasiru Yakubu Birnin Yero ne ya aiko da rahoton.