Shugabannin Kungiyar Tarayyar Turai, na duba yiwuwar kara tsawaita wa’adin ficewar Birtaniya daga tarayyar, bayan da ‘yan majalisar dokokin Birtaniyar suka haifar da tarnaki a yunkurin da Firai Minista Boris Johnson ke yi na ganin kasar ta fice daga kungiyar a ranar 31 ga watan nan na Oktoba.
Bayan da ya sha alwashin barin tarayyar a karshen watan nan “ta kowanne hali” Firai Minista Johnson, ya kuduri aniyyar ganin an yi sabon zabe, inda yayin da yake jawabi a gaban ‘yan majalisar wakilan kasar a jiya Laraba, ya ci gaba da nuna fatan ganin Birtaniyar ta fice daga kungiyar ta EU a karshen wannan wata.
“Ba na tsammanin al’umar wannan kasa za ta so a samu jinkiri, ni ma ba na son jinkirin, na kuduri aniyyar ganin mun kai ga gaci, amma, ya zama dole mu jira mu ga shawarar da kawayenmu na EU za su yanke a madadinmu.” inji Johnson.
An dai tursasa Firai Ministan ne da ya nemi kungiyar ta EU ta karawa Birtaniyar wa’adin ficewar, duk da cewa ba haka ya so ba.
Facebook Forum