Turkiyya ta ce, ba ta bukatar ta koma kai hare-hare cikin Siriya, domin Amurka ta sanar da ita cewa, Kurdawan da ke arewacin Siriyan sun kammala janyewa daga yankin.
Kasar ta Turkiyya ta fidda wannan sanarwa ce sa’o’i bayan cikar wa’adin kwanaki biyar da ta diba na tsagaita wuta a hare-haren da dakarunta suke kai wa a yankin da ake mai kallon tudun-mun-tsira ne na Kurdawa a arewacin Siriya.
Hakan na faruwa ne bayan wata ganawa da shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi da takwaran aikinsa na Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan a jiya Talata kan yadda za su samar da tsaro a kan iyakar kasar ta Siriya.
Shugaba Erdogan ya ce, “wannan zaman tattanuwa zai zama wata dama ta maido da zaman lafiya cikin gaggawa,” a yankin.
Facebook Forum