Kotun tarayya da ke Abuja, babban birnin Najeriya, ta rusa zaben fitar da gwani da jam’iyyar APC ta yi na dan takarar mukamin gwamna a jihar Taraba.
Da yake yanke hukunci a ranar Litinin, mai shari’a Obiara Afuegwa Egwualin, ya ba da umarnin a sake wani zaben fitar da gwani cikin kwanaki 14 masu zuwa.
A cewar Alkalin, ba a bi ka’ida ba wajen gudanar da zaben Sanata Emmanuel Bwacha wanda aka ayyana a matsayin wanda ya lashe zaben fiytar gwanin.
Kotun har ila yau ta ba da umarni ga Bwacha, da ya daina ayyana kansa a matsayin dan takarar mukamin gwamna karkashin tutar jam’iyyar at APC a jihar.
Sanata Yusuf A. Yusuf na daya daga cikin ‘yan takarar da ya ruga kotu don a bi masa kadi inda ya ce, ba a yi zaben fitar da gwani na kujerar gwamna a jihar Taraba ba.
A nasu bangaren, wasu daga cikin mazauna jihar Taraba irinsu Alhaji Habubakar Naira, cewa suka yi wannan al’amarin ya yi, domin dama an take ka’idojin dimokradiyya.
Su kuwa bangaren Bwacha ta bakin mai magana da yawunsa Ambasado Rikwense Muri, ya ce suna da daman daukaka kara ko kuma su shiga zaben.
Saurari cikakken rahoton Lado Salisu Garba daga Jalingo: