Sanarawar Taliban ta bayan nan ta haifar da rashin tabbas ga yarjejeniyar zaman lafiyar tsakaninta da Amurka wadda aka kulla a Qatar a makon da ya gabata.
Sanarwar na zuwa ne wuni guda bayan da wata kafar yada labarai a Amurka ta ce gwamnatin Amurka ta tattara wasu bayanan sirri cewa kungiyar ‘yan ta’addan bata da niyar cika alkauran da ta yi a yarjejeniuyar zaman lafiya ta ranar 29 ga watan Faburariru
Wata sanarwar da Taliban ta fitar yau Asabar ta hakikance cewa yayin da shugaban nata Mullah Haibatullah Akhundzada ya kasasnce babban sarki a dokance toh bai yiwuwa a samu wani shugaba a Afghanistan.
Sanarwar ta ce yakin jihadi da aka kwashe shekaru 19 ana yi karkashin babban jagoran har izuwa karshen ayyukan sojojin kasashen wajen, bai nuna mulkin nashi ya zo karshe ba, tana mai nuni da yarjejeniyar zaman lafiyar da Amurka.
Wata hadakar sojojin kasa da kasa karkashin jagorancin Amurka suka kai mamaya a Afghanistan, makwanni bayan harin ta’addanci da aka kaiwa Amurka a shekarar 2001 kana suka hambarar da mulkin Taliban bisa dalilin baiwa shugaban al-Qaida da ake zarginsa da shirya kai harin ta’addancin mafaka.
Gagagrumar yarjejeniyar da Amurka da Taliban suka kulla a gaban manyan wakilan kasashen duniya da dama, ta nuna shirin da Amurka ke yi na kawo karshen dadadden yaki da kuma aniyar kwashe sojojinta da suka kai akalla dubu 13 daga Afghanistan zuwa Washington nan da watanni 14.
Facebook Forum