Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Ta Fara Aiki a Idlib


Shugabbanin Rasha da na Turkiyya kenan yayin da suke gaisawa ranar 5 ga watan Maris, 2020.
Shugabbanin Rasha da na Turkiyya kenan yayin da suke gaisawa ranar 5 ga watan Maris, 2020.

Yarjejeniyar tsagaita wuta da shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaran aikinsa na Turkiyya suka kulla, ta fara aiki a yankin Idlib da ke arewa maso gabashin Syria.

A jiya Alhamis shugabannin biyu suka cimma matsaya bayan wata tattaunawa da aka yi a Moscow kan yadda za a sassauta hare-haren da ake kai wa a yankin.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, hare-haren da ake kai wa, za su iya jefa jama’a cikin mummunan yanayin da duniya ba ta taba gani ba.

Kelly Craft, jakada ce daga Majalisar Dinkin Duniy kuma ta ce, “kayayyakin tallafi da ake kai wa yankin, ba su ne maslahar wannan rikici ba, abu mafi muhimmanci shi ne a tsagaita wuta.”

A baya dai Rashar da Turkiyya sun sha cimma matsayar tsagaita-wuta wadanda ke rugujewa tun kafin a je ko ina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG