Amurka ta karrama wasu mata su 12 daga sassa daban-daban na duniya da lambar yabon hazikan mata ta kasa da kasa a jiya Laraba.
Matan sun sami lambobin yabon ne saboda rawar da suke takawa a fafutukar kare hakkin dan Adam, da bangaren dimokiradiyya, da daidaiton jinsi da kuma karfafa gwiwar mata.
Daya daga cikin wadanda aka karrama ita ce Sayragul Sauytbay wata ‘yar kabilar Kazakh wadda ta fallasa batun wani sansani da ake tsare fursunoni musulmai a yankin Xinjiang na kasar China.
Hazikan matan 12 da suka lashe lambar yabon a wannan shekarar, sun hada da wata 'yar jarida daga kasar Armenia, wacce ta jagoranci yaki da cin zarafin da ya shafi jinsi, da wata ‘yar jarida ‘yar kasar Bolivia, wadda ke fafutukar karfafa dimokiradiyya, da wata mai fafutukar kare hakkin tsirarun musulmai, da wata ‘yar rajin kare hakkin dan Adam a Syria, da kuma wata mai samar da kariya ga mata ‘yan gudun hijira daga Yemen.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo, ya ce, wadannan matan 12 sun zama abin koyi.”
Da take jawabi a wurin taron, uwargidan shugaban Amurka Melania Trump, ta ce, wadannan matan sun nuna irin bajintar da mata ke da ita. Kowaccensu ta nuna ayyukan karfin hali da jagoranci na gari, yawancin lokuta ma rayuwar su na tattare da hadari. Ta kara da cewa wadannan sune fuskokin gwarzayen mata na gaskiya.
Facebook Forum