Abin mamaki ga mutane da dama, Frai Minista Hun Sen dadadden shugaba a yankin Asia, ya sake lashe zabe a matsayin Frai ministan a watan da ya gabata. 'Yan adawa sun kalubalanci zaben cewa an yi sata kana ba a yi gaskiya ba wurin fitarda sakamakon zaben.
Ofishin kare hakkin bil adama na MDD ya nuna matukar damuwa ga take hakkokin bil adama a cikin lokacin zaben. Hukumar kare hakkin bil adaman tace an wargaza babbar jami’iyar adawa ta Cambodia National Rescue Party, cikin Nuwamban bara kuma madugun yan adawan na ci gaba da zaman gidan yari bisa lafin cin amanar kasa.
Mai Magana da yawun hukumar kare hakkin bil adaman Ravina Shamdasani ta fadawa Muryar Amurka cewa ana tsorarata masu adawa da zaben, ana tsangwamarsu ana kuma kama su saboda fadar albarkacin bakinsu game da zaben.
Tace ana yi musu barazanan cewa zasu sha wahala a wurin aiki na gwamnati kuma ba zasu samun aikin ba idan basu yi zabe ba. Tace mun samu bayanai cewa ana biyan mutane da suka yi zabe. Tace mun mika wadannan bayanai ga gwamnati kuma mun bayyana damuwarmu akai.
Hukumar kare hakkin bil adama ta MDD ta yi kira ga gwamnati ta sako 'yan adawa da 'yan jarida da 'yan rajin kare hakkin bil adama da ma wasu 'yan kasar da aka dauresu saboda sun fadi albarkacin bakinsu.
Facebook Forum