Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaitacen Tarihin Donald Trump Dan Takaran Shugaban Kasa Na Jam'iyyar Republican


Donald Trump dan takaran shugaban kasa a karkashin jam'iyyar Republican
Donald Trump dan takaran shugaban kasa a karkashin jam'iyyar Republican

Donald Trump attajiri ne da ya gaji tarin dukiya daga mahaifinsa, musamman dukiyar arzikin gine-gine, wanda ya tara biliyoyin daloli daga rahottanin da ake bugawa a kansa a cikin mujallu iri-iri, tauraro ne na shirye-shiryen gidajen Telbijin kuma a yanzu shine dan takaran shugaban kasa na jami’iyar Republican a zaben bana a nan Amurka.

Donald Trump ya tara dukiya mai atrin yawa daga gone-ginen binayen ofisoshi, binayen Otal otal, gidajen caca, filayen wasan kwallon golf da wasu manyan gine gine a fadin duniya. Haka kuma shine shugaban rukunin kampunnan Trump wadanda ke safarar gine ginen gidajen haya da kampunnan masana’antu hade da wasu harakokin kasuwancinsa.

An dai haife Donald Trump ne a gundumar Queens a birnin New York, kuma ya girma ne a unguwar masu hannu da shuni ta Jamaica Estates. Yana cikin ‘ya’ya biyar da da mahafinsu, Fred Trump, ya Haifa. Shi mahaifin nasu dai sanannen attajiri ne da yayi suna wajen sana’ar gine-ginen gidaje, wanda kuma hatsababben mutum ne mai son mulki, wanda kuma, bisa ga dukkan alamu, Dan nashi (Donald) ya gaje shi.

A shekarar 1968 ne Trump ya kamala karatu a babban jami’ar nazarin harkokin kudi ta Wharton. Da yake daman mahaifinsa sana’ar gine gine yake yi a gundumomin Brooklyn da Queens, Donald Trump sai ya mai da hankali wajen gudanarda irin wannan sana’ar a cikin unguwar Manhattan.

A cikin sheakrun 1970 ne ma’aikatun shari’a suka zargi ‘yan gidan Trump din da laifin keta dokokin dake hana nuna banbanci wajen baiwa mutane gidajensu na haya, inda akace basa bada gidajensu ga mutane marasa galihu da aka rinjaya hayar gidajensu. Donald Trump ya sasanta wannan batu a wajn kotuna.

Daga bisani Trump ya yi wani babban yunkuri inda ya sayi ginin wata kasaitacciyar otal da ke kusa da babbar tashar jiragen kasa ta Grand Central, sannan yaje ya ciyo bashin sama da dala miliyon 70 kuma ya tattauna da hukumomi don neman rangwamin haraji don sayen sabuwar otal din Grand Hyatt Hotel.

Sai dai watakila an fi saninsa da da gininsa na Trump Tower da ya kai dala miliyon 200 mai cike da alatu da kawa, makeken bine mai hawa 58 wanda ya kunshi gidajen zama da shagunan kece reni.

Haka kuma Trump ya shahara wurin gina gidajen caca birnin Atlantic City dake jihar New Jersey inda ya mallaki gidajen caca kamar su Trump Plaza, Trump Castle, da makeken gidan cacan nan na Taj Mahal wanda shi kadai an batarda mankudaden kudade sama da Dala Bilyan (watau milyan dubu) daya wajen girka shi.

Sai dai kuma duk karshenta, wadanan gidajen cacan sun wargaje saboda sun kasa samarda riba.

A lokacin da hada hadar kasuwancin gine gine gidaje ta huskanci rushewa a shekarar 1990, i darajar dukiyarsa ta sauko kasa daga dala biliyon daya da miliyon 700 zuwa dala miliyon 500 kawai. Karshenta ma sai da Trump ya ranci kudikumaya samo sabbin masu zuba jari don gujewa wargajewar harakokinsa na kasuwanci.

Sai dai wani abinda Trump ya kasa iya kaucewa shine yawan auratayya da kuma yawan sakin matan da yake ta aure, abinda yassa labaran yawan rigimarsa da mata tayi ta fitowqa a kafofin watsa labarai. Daya daga cikin matan da ya saka itace matarsa ta farko Ivana da suke da yaya uku dashi, wacce bayan mutuwar aurensu, ya auri Marla Maples kuma, ita ma, ya sake ta bayan wani lokaci. A shekarar 2005 Trump ya auri matarsa ta yanzu, Melania, wacce mai nunin kayan sanayawa ce kuma ‘yar kasar Slovenia.

Wani shirin gasa na telbijin mai suna “The Apprentice” ya maida Trump kamar wani gwarzo ko tauraro. Masu gasa a wannan shiri suna papatawa ne su zama manaja na kampanin Trump, kuma duk wanda ya gaza yin nasara a tambayoyi da sauran jarabawar da ake musu,sai Trump ya salleme shi da kalimomin “an kore ka.”

Wannan shiri ya samarwa Trump zunzurutun kudin da suka haya dala miliyon 200.

Trump ya soma bayyana sha’awar shiga siyasa a fili a cikin shekarun 1980., lokacinda ya shiga jami’iyar Reform Party, daga bisani ya koma Democrat, sa’annan kuma ya tsaya a matsayin independent. A cikin shekara 2012 ne Trump ya sake chanja sheka, inda ya bayyana kansa a matsayin dan jam’iyyar Republican, inda daga lokacin ne ya soma anfani da taken nan na “zamu sake maido da martabar Amurka.”

Sai dai kuma a matsayinsa na dan takara, Donald Trump ya yi kaurin suna wurin fadan kalamai na cin mutuncin jinsunan mutane daban-daban da suka hada da caccakar bakin haure yan kasar Mexico wadanda ya zarge su da cewa wai suna shigowa da miyagun kwayoyi da matsaloli a nan Amurka. Haka kuma yace zai gina wata katafaren Katanga akan iyakar Amurka da Mexico wanda kuma yacekasar Mexicon ce zata biya kudin aikin gina katangar.

Trump yaci gaba da magangannun tsokana da sukar lamirin mutane iri-iri, ciki da cewa wai zai haramtawa Musulmi shigowa Amurka biyo bayan wani harbi da aka yi a California, inda aka yi asaran rayukka.

Amma duk da wannan katobara da tabargazan dake fitowa bakinsa, goyon bayansa sai dada hauhawa yake a tsakanin yan jami’iyarsu ta Republican wanda suka dogara a kansa ya kirkiro ayyukan yi ga Amurkawa.

Amurkawa da yawa dai sun cimma matsayar cewa wannan zaben shugaban kasa, zabe ne da ba’a taba irinsa ba a tarihin kasar tasu.

Wannan zabe ne inda ake papatawar tsakanin dan jami’iyar Republican wanda mutum ne mai yawan kalaman dake jan hankalin jama’a wato Donald Trump da kuma, a daya gefen, wata mace wacce tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka ce kuma tsohuwar uwargidan shubana kasa, Hillary Clinton.

Wannan zabe ne dake cike da tsrakakiya wanda jama’a ko a mafarki basu zaci cewa hakan zasu fuskanta ba.

Ga fasarar Baba Yakubu Makeri

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:00 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG