Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaddama Tsakanin Amurka Da Iran


Jirgin leken asirin Amurka maras matuki
Jirgin leken asirin Amurka maras matuki

Saura kiris Amurka da Iran su gwabza jiya Alhamis bayan da aka kakkabo jirgin sintirin Amurka mara matuki mai suna Global Hawk a yankin ruwan Hormuz, al'amarin da Shugaban Amurka Donald Trump ya kira "mummunan kuskure."

“Wannan wani sabon koma baya ne,” abin da Trump ya fada wa manema labarai kenan a jiya Alhamis a lokacin da ya ke ganawa da firai ministan kasar Canada, Justin Trudeau a fadar White House.

Shugaba Trump ya kara da cewa wannan jirgin saman ya ratsa yankin ruwa na kasa da kasa ne. kuma muna da shaida a rubuce, ya kara nanata wa manema labaran cewa za ku ji anan gaba idan Amurka ta maida martani.

Amma Iran, tace jirgin ya bi hanyar da bai kamata ba kuma ya karya dokar kasa da kasa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG