Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Indomi Zata Maidani Babban Likita a Rayuwata


Auwalu Isyaku Mai Indomi
Auwalu Isyaku Mai Indomi

Matasa ku tashi ku kama sana’a, kada ku kasance cikin zaman banza, wani matashi dan shekaru gomasha biyar 15, Auwalu Isyaku, ya nema ma kanshi sana’a don ya tsare ma kansa lalurar yau da kullun.

Shidai Auwalu, yana karatu a makarantar sakandire ne inda yake aji JSS 2, yakanje wajen da yake aiki da safe yayi wanke-wanke da kuma kaima mabukata Indomi da abunsha, yana dai aiki karkashin ubangidanshi ne, wanda daga bisani kamar karfe gomasha biyu na rana, yakan tafi makaranta.

Yana hada karatu da aiki wanda kowanne nada lokacinsa, yakan yi amfani da kudin daya tara wajen sayama kanshi abun da yake da bukata batare da ya jira mahaifansa sun yi masa ba, babban buri Auwalu, shine yazama babban likita, yasamu nashi asibiti da zai dinga taimaka ma al’uma.

Babban abun sha’awa a nan shine, yakamata ace yara matasa su kasance suna da tunanin mai sukeso su zama a nan gaba, idan Allah yasa sun girma, abun da yakamata ace iyaye suna ma ‘yayansu tun suna ‘yan kanana, shine su nuna musu hanyoyin zama wasu abu a rayuwa ba kawai su kyalesu kara zube ba, su sani da cewar duk abun da sukeso su zama a rayuwa zasu iya zama idan sun sa kansu.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG