A Najeriya, takaddama ta kunno kai a tsakanin Mahukunta da Kungiyoyi masu zaman Kansu da ‘yan siyasa akan batun soke zababbun Shugabanin Kananan Hukumomi sanan a maye gurbinsu da shugabanin rikon kwarya, inda suka ce za su dauki mataki don gaggauta sauya dokar da ta kafa kananan hukumomin.
Wanan takaddamar ta samo asali ne daga wasikar da Atoni Janar na kasa ya aika wa wani Gwamnan jihar Kudu maso yama akan cire zababbun Shugabanin Kananan hukumomi sanan ya nada na rikon Kwarya.
Abin da ya dauki hankalin Kungiyoyi masu zaman kansu, kamar su Shugaban Kungiyar “Save Da Change” Alhaji Bashir Dan Musa, wanda ya bayyana ra'ayinsa cewa a gaggauta gyara kundin tsarin mulkin kasa domin a bai wa kananan hukumomin damar yi wa talaka aiki, saboda su ne suke kusa da al'umma masu kada kuri'a a lokacin zabe.
Wani Masanin Kimiyar zamantakewar dan Adam kuma malami a Jami'ar Abuja, Dokta Abubakar Umar Kari, yana ganin an dade ana wannan Ja-in-ja akan batun hukumomin, amma laifin na kundin tsarin mulki ne, sanan kuma akwai wadanda ke goyon bayan ba wa kananan hukumomin ‘yancinsu, kuma akwai wadanda ke goyon bayan Gwamnoni, wadanda suke wa yunkurin ‘yancin kananan hukumomin kafar angulu.
Saurari cikakken rahoton wakiliyar Muryar Amurka, Medina Dauda.
Facebook Forum