Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kashe Matashi Dan Afrika A Amurka Ya Haifar Da Zanga Zanga


MUBARAK SULEMAN 2
MUBARAK SULEMAN 2

A ranar Laraba cikin dare ne ‘yan sandan jihar Connecticut na nan Amurka suka harbe Mubarak mai sheakru 19 da haifuwa yayin da ya dauki wata mota ya arce da ita. Bayan an kira ‘yan sanda da suka kwashe mintoci suna binsa daga karshe suka bude wuta suka harbe shi har sau bakwai.

Mahaifiyar Mubarak Suleman, Hajia Humu Morla mai rike da sarautar magajiya a birnin New York ta mana karin bayani a kan batun. Tace danta Mubarak yana fama da rashin lafiya da ya shafi kwakwalwarsa kuma lokaci lokaci ciwon ya kan tashi. Lamarin da ya samu kansa ke nan a lokacin da ya tafi ya dauki motar wani da yasa aka kira masa ‘yan sanda.

Labarin ya dauke hankalin al’ummar birnin New Haven a Connecticut lamarin da ya haddasa zanga zangar da ta kunshi jinsinan fata da matasa masu yawa.

A wurin zanga zangar ne shugabannin addinai suka yi kira da tabbatar da adalci ga wannan matashi da aka harbe shi har lahira, kamar yanda Track Ari na cibiyar huldar kungiyoyi Musulmin Amurka shiyar Connecticut ya fada.

“Yace dole ne a gudanar da bincike kuma bincike na gaskiya kuma duk wanda aka samu da laifi yakamata a hukunta shi”.

Yayinda yake jawabi da masu zanga zangar magajin garin New Haven na jihar Connecticut Justin Elicker yayi alkawarin daukar matakin tabbatar da adalci.

“Yace na kira kwamishinan kula da kare jama’a kuma na nuna masa damuwa a kan wannan batu kuma na bukaci mu gana domin magance aukuwan irin haka nan gaba ya kuma jajantawa iyalain marigayi”.

Ga dai Karin bayani cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:23 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG