Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Ta Kai Hari Biu


Wasu da suka gudu daga jigajensu.
Wasu da suka gudu daga jigajensu.

A daren Lahadi ne wasu mahara da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai hari akan garin Burate dake cikin karamar hukumar Biu a jihar Borno.

'Yan Boko Haram din sun kona wata makarantar firamare da raunata wasu jami'an soja guda uku.

Wannan harin ya zo ne bayan kwana daya da wasu jami'an soja suka kaiwa 'yan bindigan hari a wani kauye da ake kira Kawori dake cikin karamar hukumar Kondiga inda suka hallaka 'yan bindigan fiye da hamsin. Sojojin sun kuma kwato wasu muggan makamai masu dimbin yawa da suka hada da wasu guda biyu da ake harbo jiragen sama dasu.

Hakazalika bayyanan dake fitowa daga garin Buraten sun nuna cewa maharan da dama sun gamu da ajalinsu sakamakon gaba da gaba da suka yi jami'an tsaro.

Alhaji Maina Garga hakimin garin Burate ya shaidawa Muryar Amurka yadda lamarin ya faru. Yace maharan sun shiga garin ne kamar karfe goma da rabi nan take kuma suka fara harbe-harbe. Sun kai wajen awa uku suna harbi. Da sojoji suka fi karfinsu sai suka gudu. Lokacin da suke fita daga garin suka kone makarantar firamare. Maharan sun zo kan babura da motocin hilux biyu. Wasu mutanen garin sun gudu sun shiga daji.

Duk da nasarar da sojoji ke samu jama'a da dama na kauracewa kauyukansu suna shiga cikin manyan birane.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG