A nata bangaren, majalisar dattawa ta amince da dokar amma ta ce dole sojoji su kiyaye lafiyar talakawa. Kada su matsa masu. Kada su taba wadanda basu ji ba basu gani ba.
Sanato Bindoji Birila daga jihar Adamawa, daya daga cikin jihohin dake karkashin dokar ya yi magana da yawun 'yan majalisar dattawa inda ya shaidawa wakiliyarmu cewa bakinsu yazo daya kan lallai jami’an tsaro su yi kafa-kafa kada su kuskura su maimaita irin abun da ya faru a garin Baga.
Yace talakawa ne suka zabesu, dole ne kuma su tashi tsaye su karesu. Yace ba zasu yadda a gallaza ma talakawa ba.
Kodayake majalisar wakilai ita ma ta amince da dokar amma tace shugaban kasa bashi da ikon ba gwamnonin jihohin da ya ayana wa dokar, shawarori akan yadda zasu gudanar da mulkinsu kamar yadda ya sa a dokar.
Maimagana da yawun 'yan Majalisun, Ibrahim El-Sud yace shugaban na iya basu shawara kan abubuwan da suka shafi tsaro kawai.
Yace sun yi kashedin kada shugaban ya yi ma gwamnoni kasalandan dangane da yadda suke gudanar da mulkin johohinsu.
Wakiliyarmu Madina Dauda ta yi karin bayani a rahoton da ta aiko mana.