WASHINGTON, DC —
Kwamitin sasanta gwamnatin Najeriya da ‘yan kungiyar Boko Haram ya gabatar da bukatar cewa gwamnati ta saki mata da yaran da ke tsare bisa zargin su da zama ‘yan kungiyar. A kan wannan batu, Ibrahim Ka’almasih Garba ya tattauna da Dakta Kabir Mato, masanin ilimin kimiyar siyasa a jami’ar Abuja, wanda ya fara da cewa, "da ma daya daga cikin irin manya-manyan larurorin da ake fuskanta ya ta’allak’a ne ga irin yadda gwamnatin Najeriya ta ke yin kunnen k’ashi bisa ga shawarwari da ake ba ta a kan yadda za a yi maganin wannan tashin hankali cikin lumana, har aka kai wannan matsayi da aka kafa wannan kwamiti na neman afuwa da kuma zuwa dokar ta baci da aka aiwata a wadannan jahohi guda uku". Dakta Kabir Mato ya ce ya na ganin ga dukan alamu sakin wadanda ke tsare din zai taimaka sosai tun da wannan ya fito ne daga shawarwarin da ‘yan kwamiti su ka baiwa gwamnatin tarayya, da shugaban kasa kuma har ya amince da shi. Sannan Dakta Kabir Mato ya ci gaba da cewa:
Dr. Kabir Mato ya ce, da ma, matsalar ta danganta ne da yadda gwamnati ke kin jin shawarwarin da ake ba ta game da rikicin Boko Haram