Hukumar tsaron lafiyar jama’a wato “Civil Defence Corps” reshen jahar Enugu, ta cafke wata mata mai suna Nkechi Isioko, a lokacin da take kokarin sayarda jaririn ta ga wata Mrs. Blessing Egbo.
A cewar ita Nkechi, wace ake zargi da kokarin sayar da jaririyar ta ce ta fara karabar Naira 10,000, a matsayin kafin alkalami da bisani Mrs. Egbo, ta cikie mata sauran kudin.
Ta ce dalilin sayarda jaririyar shine domin tana bukatar kudin ne domin yiwa kanta magani, amma a cewar ta bayan da aka ba ta shawarar kada ta sayarda da jaririyar sai ta maidawa Mrs. Blessing Egbo, kudin ta.
Shugaban hukumar ta “Civil Defence” a jahar Mr. Lar Stephen Zwali, ya shawarcin masu sana’ar fataucin mutane da karuwai da su canza sana’a, idan bahaka zasu sa kafar wando daya.