Fatima Rabiu yar asalin garin Babura ce, a Jihar Jigawa Najeriya. Daliba ce mai karatun digiri na biyu a fannin kasuwanci a jami’ar jihar Minnesota ta nan kasar Amurka. Matsayi ta, na kasanchewa daliba a makarantar da ke kunshe da dalibai daga kasashe masu dama a duniya, ta fuskanci wadansu irin matsaloli da suka shafi fanni da daman, kadan daga cikin su kuwa sune.
Matsalolin da ta fuskanta yayin karatu a Amurka, suna da dan dama, misali kamar sauyin yanayi, gaskiya ya banbanta da yanayin gida Najeriya, wanda ta saba da shi. Yanayin rani, da damina da ake da su can a gida ya sha banban da irin yanayin da ke da a nan kasar. A nan yanyanin sun rabu kashi uku, amma yanayin da yafi daga hankali shine “winter” a tuance, hunturu mai kankara da sanyi sosai .
Al’adu da dabi’un mutanen Amurka, sun banban ta sosai idan aka kwatanta su da namu na gargajiya. Alal-misali irire iriren abinci su da kuma yanayin zaman takewan su sun banbanta kwarai da gaske.