‘Yan wasan Los Angeles Rams sun doke takwarorinsu na Cincinnati Bengals da ci 23-20 a wasan karshe na Super Bowl a gasar kwallon kafar zari-ruga ta NFL a Amurka.
Wannan shi ne karo na biyu da Rams take lashe kofin a tarihin kungiyar kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
An buga wasan ne a filin wasa na Los Angeles Meomorial Colesium da ke birnin Los Angeles.
Rabon da kungiyar ta Rams ta lashe kofin gasar ta Super Bowl tun shekaru 22 da suka gabata a lokacin tana St. Louis.
Wannan nasara na nufin kungiyar ta bi sahun Tampa Bay Buccaneers a matsayin kungiyoyi biyu kacal da suka lashe gasar a gida.
A bara Buccaneers ce ta lashe kofin gasar.
Dan wasan Rams Cooper Kupp ya kai kwallo biyu ga gaci, ciki har da wacce ta kai ga lashe wasan daga hannun Matthew Stafford a zagaye na hudu.
Kazalika Aaron Donald ya yi wasan kura da mai tsaron bayan Bengals Joe Burrow inda shi ma ya cimma kwallonsa da ta kai ga nasarar kungiyarsu.
Kusan mutum miliyan 100 aka yi kiyasin sun kalli wasan na Super Bowl a akwatunan talabijin a Amurka.