Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buccaneers Ta Lashe Kofin Super Bowl


Yayin karawar da aka yi tsakanin Buccaneers da Kansas Chiefs a ranar Lahadi
Yayin karawar da aka yi tsakanin Buccaneers da Kansas Chiefs a ranar Lahadi

Kungiyar Tampa Bay Buccaneers a Amurka, ta lashe kofin gasar NFL a wasan karshe na Super Bowl a Amurka.

Buccaneers ta samu nasarar ne bayan da ta doke Kansas Chiefs da ci 31-9 wacce ita ke rike da kofin gasar.

Wannan wasa shi ya kasance mai mafi karancin ‘yan kallo a tarihin gasar saboda annobar coronavirus.

Ita dai Buccaneers ita ce kungiyar ta farko da ta buga wannan wasa na Super Bowl a filin wasanta na gida.

Burin Chiefs na zama kungiya ta farko da ta lashe kofin a karo na biyu a jere ya she ruwa.

Wasan dai ya nuna irin kwarewar da Buccaneers ke da shi wajen iya tsare gida duk da irin namijin kokarin da Chiefs ta yi na ganin kai ga gaci.

Hukumar da ke kula da gasar NFL, ta bar ‘yan wasa 25,000 ne kacal suka shiga filin mai daukan mutum 65,000.

An dai cike sauran filin ne da kwalaye dubu 30, 000 na masu goyon kungiyoyi.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG