Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sultan Ya Samu Gagarumar Tarba A Sakkwato


Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar
Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar

Yayin da ake dakon majalisar dokokin jihar Sakkwato ta yi matsaya akan kudurin dokar nan da ya jawo ce-ce-ku-ce a kan batun masarautar Mai alfarma Sarkin Musulmi, jama’a na ci gaba da nuna goyon baya ga masarautar.

Wannan ba ya rasa nasaba da gagarumar tarbo da aka yi wa Sarkin Musulmin bayan da ya dawo gida a ranar Alhamis.

An jima ana korafi a kan rashin bai wa Sarakuna dama a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya duk da muhimmancin da suke da shi a cikin al'umma.

Sai dai duk da sanin muhimmancin sarakuna bai hana wasu Gwamnatoci taba masarautu ba musamman a arewacin najeriya, inda a baya-bayan nan gwamnatin Sakkwato take kokarin gyara ga dokar da za ta shafi nadin sarautu, abin da tuni ya janyo ce-ce-ku-ce, duk da yake gwamnatin ta ce tsarin da ma haka yake a baya.


Ita kanta masarautar Sarkin Musulmi ta bakin wakilinta a wurin sauraren ra’ayoyin jama’a akan dokar, Sa’in Daular Usmaniya, Muhammad Jabbi Kilgori ta ce a shirye take ta yi aiki da sabon tsarin domin da ma ta saba da shi.

Sai dai har yanzu jama’a ba su karbi wannan tayi na gwamnati ba akan gyaran dokar domin suna ganin taba martabar gidan Dan Fodiyo ne.

Jama’a ne suka yi cincirindo a hanyar shiga fadar Sarkin Musulmi suna yi masa maraba, Kamar yadda aka yi ta yada hotonan a kafafen sadarwa na yanar gizo.

Tuni dai da majalisar dokokin jihar Sakkwato ta yi nisa da aiki akan gyaran dokar kuma kowane lokaci tana iya yin matsaya a kan ta.

Makonnin da suka gabata manyan masarautu a Najeriya sun tsinci kansu cikin wani yanayi na halin tsaka mai wuya inda wasu na matakin Shari'a wasu kuma naa jiran su ga yadda Allah zai yi da su.

Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:

Sultan Ya Samu Gagarumar Tarba A Sakkwato
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:38 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG