Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Sokoto Ta Musanta Zargin Shirin Tube Sarkin Musulmi


Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III
Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III

Wata Sanarwa dauke da sa hannun hadimin gwamnan jihar Sokoto akan harkokin yada labarai, Abubakar Bawa, ya musanta zargin ya kuma ce hakan na neman kawo cikas ga alakar da ke tsakanin gwamnatin jihar da fadar Sarkin Musulmi.

Gwamnatin jihar Sokoto ta musanta zargin da kungiyar kare hakkin musulmi ta (MURIC) ta yin a Shirin tube sarkin musulmi Mai Alfarma Muhammad Sa’ad Abubakar III.

Wata Sanarwa dauke da sa hannun hadimin gwamnan jihar Sokoto akan harkokin yada labarai, Abubakar Bawa, ya musanta zargin ya kuma ce hakan na neman kawo cikas ga alakar da ke tsakanin gwamnatin jihar da fadar Sarkin Musulmi.

A jiya Litinin ne kungiyar MURIC ta yi ikirarin cewa gwamnatin jihar Sokoto na Shirin tube sarkin Musulmi.

Babban daraktan kungiyar MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ne ya bayyana damuwar a cikin sanarwar daya fitar inda yace al'ummar Musulmin Najeriya ba zasu amince da duk wani tunani na tube Sarkin Musulmi ba.

Y ace “Rade-radin dake yawo na nuni da cewar gwamnan na dira kan Sarkin Musulmin a kowane lokaci daga yanzu ta hanyar bada uzurin da yayi amfani dashi wajen cire sarakunan gargajiya 15 da yayi a baya.

"MURIC ta baiwa gwamnan shawarar cewar ya duba kafin ya sara. Kujerar Sarkin Musulmi ta zarta ta al'ada. Kujera ce ta addini. Kuma hurumin sarkin ya zarta iya kasar Sokoto. Hurumi ne daya karade fadin Najeriya. Shine jagoran addinin ilahirin Musulmin kasar.", a cewarsa.

Hakazalika da ya ke bayani a taron kolin zaman lafiya da tsaro a jihohin arewa maso yammacin Najeriya dake gudana a jihar Katsina Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya shaidawa gwamnatin jihar Sokoto cewar wajibi ne a girmama Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar, iya girmamawa .

A cewarsa "ga Mataimakin Gwamnan Sokoto, ina da dan sakon da zan baka. eh! na yarda ana cewa Sarkin Musulmin Sokoto, saidai martabarsa ta zarta hakan, shi sarki ne dake wakiltar akida. Shi wata hukuma ce daya kamata dukkaninmu a kasar nan mu martaba iya martabawa tare da bashi kariya da bunkasawa da alkintawa da kuma tallata mutuncinsa a idon duniya.

Mataimakin gwamnan Sokoton ya bayyana zargin na kungiyar MURIC a matsayin marasa tushe, ya kuma tabbatar wa al’ummar musulmi cewa ba wani shiri na tube Sarkin Musulmi.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG