Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sudan ta Kudu ta zargi Sudan da kai mata hari ta jirgin sama


Shugaban Sudan Umar al-Bashir
Shugaban Sudan Umar al-Bashir

Sudan ta Kudu ta zargi makwabciyarta kasar Sudan

Sudan ta Kudu ta zargi makwabciyarta kasar Sudan da laifin kai hari ta sama a kan wani garin da ake takaddama kai a bakin iyakarsu, kwanaki biyu kacal a bayan da kasashen suka rattaba hannu a kan yarjejeniyar hana kai farmaki kan juna.

Hukumomi a Sudan ta Kudu sun ce wasu jirage samfurin Antonov kirar kasar Rasha sun jefa bama-bamai da dama ranar lahadi a kan garin Jau, suka raunata mutane akalla hudu.

Sudan ta Kudu tana ikirarin cewa garin jau yana cikin jiharta ta Unity, yayin da Sudan ta ce wannan gari yana cikin jiharta ta Kordofan ta Kudu ne.

Rashin jituwa kan iyaka da kuma arzikin man fetur ya kara zaman tankiya a tsakanin kasashen biyu na Sudan, yayin da shugabannin sassan suke fadin cewa tana yiwuwa su koma bakin yaki.

A ranar jumma’a, wata tawagar shiga tsakani ta Kasashen Tarayyar Kungiyar Afirka ta lallashi sassan biyu sun sanya hannu a kan yarjejeniyar cewa ba zasu kai farmaki kan juna ba. Kasashen biyu su na zargin juna da goyon bayan ‘yan tawayen kasashensu, yayin da Kudu ta ce arewa ta kai hare-haren bam sau da dama cikin yankinta.

Kasashen Tarayyar Kungiyar Afirka tana karbar bakuncin tattaunawa tsakanin sassan biyu a birnin Addis Ababa, game da batun kudaden shiga na man fetur, kudaden da su ne manyan hanyoyin samun kudi na kasashen.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG