Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun kasa da kasa zata yanke hukumcin a shari'ar Charles Taylor


Tsohon shugaban kasar LiberiaCharles Taylor
Tsohon shugaban kasar LiberiaCharles Taylor

Kotun dake shari’ar tsohon shugaba Charles Taylor na Liberiya bisa laifuffukan yaki ta ce zata yanke hukumcinta a wata mai zuwa.

Kotun dake shari’ar tsohon shugaba Charles Taylor na Liberiya bisa laifuffukan yaki ta ce zata yanke hukumcinta a wata mai zuwa.

Kotun Majalisar Dinkin Duniya ta musamman mai bin bahasin laifuffukan yaki a kasar Saliyo, ta fada yau alhamis cewa a ranar 26 ga watan Afrilu ne zata yanke hukumci a kan ko ta samu Charles Taylor da laifi ko a’a, dangane da tuhume-tuhume guda 11 da ake yi masa na kisan kai, fyade, daukar yara aikin soja da wasu laifuffukan.

Ana zargin Taylor da laifin samar da makamai ga ‘yan tawaye a lokacin yakin basasar Saliyo, su kuma su na biyansa da duwatsun Daiman. Ana zargin ‘yan tawayen da laifin kashewa da sare gabobin dubban fararen hula a lokacin yakin na shekaru 11.

Taylor ya musanta aikata ko da guda daya daga cikin wadannan laifuffuka. Idan aka same shi da laifi yana iya shafe tsawon rayuwarsa a gidan kurkuku.

Wannan shari’a da aka kammala shekara guda da ta shige, an shafe shekaru uku da watanni ana yinta, inda aka saurari shaidu fiye da 110.

Taylor da masu gabatar da kara su na da ikon daukaka karar duk hukumcin da wannan kotu zata yanke.

XS
SM
MD
LG