To saidai 'yan adawa da kungiyoyo masu zaman kansu na shakkar ikirarin Shugaban. Mallam Nabilu Rabiu na jam'iyyar MNSD Nasara ya ce alkawrin da Shugaban ya yi na gudanar da wasu muhimman ayyukan yaudra ce kawai ta siyasa saboda ya ga lokacin zabe na gabatowa. Mallam Rabiu ya ce ko Amurka ba za ta iya aiwatar da abin da Shugaba Janhuriyar Nijar din ya ce zai aiwatar cikin shekara guda ba.
Shi ma shugaban wata kungiyar matasa mai suna Lawwali Tsalha ya ce ya kamata Shugaban ya yi gaskiya da kuma kokarin hada kan 'yan kasar; su kuma 'yan adawa su yi gaskiya wajen sukar manufofin gwamnati saboda kasar ta amfana. Shi kuwa wani dan kungiyar rajin yaki da cin hanci da rashawa mai suna Dauda Tankama ya ce yakar rashawa da cin hancin da Shugaba Issuhu ya ce zai yi burga ce kawai saboda tun daga kwaloluwa ake tafka almundahana a kasar.