Ministan Tsaro na Najeriya Mansur Dan Ali, wanda dan asalin jihar Zamfara ne, ya fito karara ya bayyana zargin hannun wasu sarakuna a hura wutar ayyukan kai hare-hare da kisan jama’a da kuma satar mutane domin karbar kudin fansa da ya zama ruwan dare a jihar ta Zamfara.
Wannan lamari dai ya ci gaba da jan hankalin manazarta lamurran yau da kullum, har suke ganin biri yayi kama da mutum.
Bashar Altine Guyawa shine shugaban wata kungiyar rajin kare hakkin bil adama ta Rundunar Adalci, kuma mai sharhi ne akan al’amuran yau da kullum.
Inda ya ce akwai manyan ‘yan siyasa da suka yi aiki a wasu wuraren shari’a daban-daban, yanzu haka wasu na jihar Zamfara an basu sarauta.
To sai dai kuma gwamnatin jihar ta Zamfara ma ta tabbatar da wannan zargin, inda ta ce tana daukar matakai akan wannan al’amarin, ta bakin kwamishinan lamurran kananan hukumomi na jihar, Bello Muhammad Dankande.
Tuni dai babban Sufeto-Janar na ‘Yan sandan Najeriya ya ziyarci jihar ta Zamfara, kwanaki 2 bayan ba da sanarwar dakatar da dukkan ayyukan hako ma’adinai a jihar, inda kuma ya yi taro da sarakunan gargajiya na jihar, tare da zimmar samo bakin zaren warware kalubalen.
Domin karin bayani saurari rahotan Murtala Faruk Sanyinna.
Facebook Forum