Sojojin kasar Sudan, sun hambarar da gwamnatin shugaba Omar al-Bashir bayan watannin da aka kwashe ana zanga-zanga a kasar akan mulkin sa, da ya yi tsawon shekaru 30.
A wata sanarwa ta kasa da kasa, a yau Alhamis, ministan tsaron kasar Sudan, Awad Mohamed Ahmed Ibn Auf, ya ce, an kama shugaba al-Bashir, kuma an kai shi wani wuri mai tsaro.
Ya ce sojojin kasar, sun ayyana dokar ta baci kuma sun kafa wani kwamiti wanda zai gudanar da harkokin gwamnati har tsawon shekaru biyu. Ministan ya kuma kara da cewa, an rushe dukkan gwamnatocin jihohi.
Da farko, wani sojan Sudan, ya fadawa muryar Amurka, cewa, ana tsare da Al-Bashir, dan shekaru 75,a gidan sa. Bisa ga cewar sa, shugabannin siyasa, suna tattaunawa ne, don kafa gwamnatin rikon kwarya.
Dubban mutane sun hau kan titunan birnin Khartoum a yau Alhamis, suna shagali, da raye raye, da kuma wakoki akan hambarar da gwamnatin shugaban.
Facebook Forum