Yayin da matsalar sace mutane don a samu kudin fansa ke karuwa tamkar wutar daji, wani dan jarida wanda ya samu kubuta da kyar wato bayan ganin abubuwan tayar da hankali da ya gani kafin a fanshe shi, ya yi kira ga hukumomin Najeriya da su tashi haikan wajen magance wannan matsala ta sace mutane ana raba su da dukiyarsu da ma na ‘yan’uwansu da sunan kudin fansa.
Ganin yadda aka yi ta sace mutane a ‘yan kwanakin nan, ciki har da wanda ya faru a makon jiya a hanyar Abuja zuwa Kaduna dan jaridar kamfanin yada labarai na Daily Trust mai suna Ahmed Garba ya yi bayani mai karkada hanji na irin tsawon tafiyar da su ka yi a cikin kungurumin daji, inda kafin su isa wurin da aka boye su sai da su ka shafe sa’o’i hudu su na ta shafe tafiya cikin dajin Allah.
Y ace wadanda su ka sace sun sun ce gwargwadon saurin kawo kudin fansarsu gwargwadon saurin sakinsu. Y ace da farko an bukaci Naira miliyan 100 saboda ya na danjarida wanda ‘yan jaridan Najeriya ba su sukar gwamnati idan su ka kashe su masu satar nutanen. Y ace sannu a hankali su ka rage kudin fansar zuwa 10.
Ahmed ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su tashi haikan wajen yin duk abin da ya wajaba don ganin karshen wannan bala’in. Ya yi nuni da yadda jama’a su ka fara tunanin daukar doka a hannu, da cewa muddun gwamnati ta kasa yin wani abu to wata mummunar rigimar kuma na iya tashi.
Shi ma wani dan majalisar wakilan Najeriya, Mansur Ali Mashi ya yi bayanin yadda wasu ‘yansanda su ka gaza kai dauki lokacin da irin wadannan miyagun su ka harbe wata mace. Yan a mai kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya tashi tsaye.
Ga wakilinmu Sale Shehu Ashaka da cikakken rahoton:
Facebook Forum