Hakan wani bore ga abinda ma’aikatan suka bayyana da sabawa ka’idojin aikin gwamnati, sakamakon nade-naden da gwamnati ta yiwa ‘yan siyasa a matsayin manyan daraktoci a ma’aikatun gwamnatin jihar.
Kafafen yada labarai na cikin gida sun ruwaito cewa rufe kofofin ofisoshin da manyan kwaduna, har ma da asibitocin dake ilahirin kananan hukumomin jihar neja 25.
Tun da fari, gwamnan jihar Neja, Umar Bago ya nada mutane da dama a matsayin manyan daraktoci a bangarorin hada-hadar kudi da mulki da ayyuka harma da ciyamomin da mambobi da kwamishinonin dindindin a hukumar kula da kananan hukumomin jihar da makamantan hakan.
A sanarwar da ta fitar tunda fari ta hannun Sakataren Gwamnatin Jihar, Abubakar Usman, gwamnatin Nejar tace an gudanar da wani taro da Hadaddiyar Kungiyar Kwadagon a ranar 20 ga watan Fabrairun da muke ciki da nufin kaucewa shiga yajin aikin.
Sai dai a jiya Talata, kungiyar kwadagon ta musanta batun ganawa da wani jami’in gwamnati akan batun.
Dandalin Mu Tattauna