Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Somalia Ta Zargin Sojojin Kungiyar Afirka Na Kiyaye Zaman Lafiya da Kashe Fararen Hula Goma


Sojojin Kungiyar Kasashen Afirka dake aikin kiyaye zaman lafiya a Somalia
Sojojin Kungiyar Kasashen Afirka dake aikin kiyaye zaman lafiya a Somalia

Jami’an kasar Somaliya sun zargi sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar kasashen Afrika da laifin kashe farar hula goma sha daya a al’amurra dabam dabam guda biyu da suka auku a karshen mako.

Gwamnan yankin Shabelle Ibrahim Aden Najah ya fadawa sashen Samaliya nan nan Muryar Amirka cewa wani tankin yaki mallakin sojojin kiyaye zaman lafiya, jiya Lahadi da dare yabi ta kan wasu gidaje bayan da ya taka nakiyar da aka bizne a karkshin kasa. Yace wata mace da yayanta guda uku aka kashe. A saboda haka ya bukaci ofishin sojojin ya gudanar da bincike.

A ranar Asabar sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar kasashen Afrika da ake cewa AMISOM a takaice suka bude wuta akan wata mota suka kashe fara hula shidda.

Gwamnan yace ofishin AMISOM a Somaliya ya fada masa cewa sojojin suna sintiri ne a lokacinda suka yi kicibis da motar. Suna tsamani motar tana dankare da nakiyoyi shi yasa suka bude mata wuta.

Ofishin AMISOM bai maida martini ga wannan zargi ba. Su dai sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar kasashen Afrika suna Somaliya ne domin su taimaka wajen daukan matakan tsaro da horar da sojojin Somaliya da kuma taimakawa sojojin kasar a fafatawa da yan yakin sa kan kungiyar Al Shabab.

XS
SM
MD
LG