Wasu matasa a karamar hukumar Tangaza da ke jihar Sokoto a arewa maso yammcin Najeriya, sun kashe wasu mutane da ake zargin cewa ‘yan bindiga ne.
Rahotanni na cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar inda matasan cike da fushi suka kutsa kai cikin hedkwatar ‘yan sandan yankin na Tangaza suka zakulo ‘yan bindigar suka kashe su tare da cinna musu wuta.
Jaridar Daily Trust ta ce ‘yan bindiga 13 aka kashe yayin da Channels ya ce mutum 6 ne.
Bayanai sun yi nuni da cewa lamarin ya samo asalin ne bayan da jami’an tsaro suka kamo wasu ‘yan bindiga da ake zargi da kai wani hari a ranar Juma’a wanda ya yi sanadin mutuwar mutum biyu a yankin Tangazan.
A cewar rahotanni, baya ga kashe mutum biyu da ‘yan bindigar suka yi sun kuma sace kayan abinci dama a wani shigo.
Hakan ya sa jami’an tsaron suka shiga cikin dajin don yin farautar ‘yan fashin dajin, inda suka yi nasarar kamo ‘yan bindigar da dama tare da kayan abincin da suka sace.
Bayanai sun yi nunu da cewa an kulle ‘yan bindigar a ofishin ‘yan sanda bayan da aka kama su, amma matasan cikin fushi wadanda yawansu ya sa suka fi karfin jami’an ‘yan sandan, sun kutsa kai cikin hedkwatar ‘yan sandan suka kashe ‘yan bindigar tare da kona su.
Jihar Sokoto na daga cikin jihohin da ke yawan fama da matsalar hare-haren ‘yan fashin daji, wadanda suke kashe mutane su kuma saci jama’a don neman kudin fansa.