Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Kashe Mataimakin Turji Da Wasu Mayakansa Da Dama


Sojojin saman Najeriya
Sojojin saman Najeriya

Dakarun rundunar tabbatar da tsaro a yankin Arewa maso yammancin Najeriya da ake kira ‘Operation Fansan Yamma’ sun yi wa mayakan ‘yan ta’adda da Bello Turji ke jagoranta ragaraga.

Sojojin sun yi nasarar kashe babban mataimakin Turji, Aminu Kanawa, da wasu manyan kwamandoji da dama a wasu jerin hare-haren da suka kai masu a tsakanin ranakun 20 zuwa 21 ga watan Janairun 2025.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da ta fito daga hannun Manjo Janar Edward Buba, daraktan yada labarai na rundunar tsaron Najeriya a madadin babban hafsan sojin kasar.

Ya ce, hare-haren da aka kai wa sansanoni a jihohin Zamfara da Sakkwato, sun kuma yi sanadiyyar raunata makusantan Turji da suka hada da kaninsa Dosso da kuma babban abokinsa Danbokolo.

Daga cikin manyan kwamandojin da aka kashe akwai Abu Dan Shehu, Jabbi Dogo, Dan Kane, Basiru Yellow, Kabiru Gebe, Bello Buba, da Dan Inna Kahon-Saniya-Ya-fi-Bahaushe.

Bugu da kari, sojojin sun ce sun kashe ‘yan ta’adda sama da 24 wanda suka tsere daga sansanonin Turji da ke yankin Gebe a Karamar hukumor Isa ta jihar Sakkwato da Gidan Rijiya a karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.

Har ila yau Manjo Janar Buba ya ce dakarun sojin sun kuma kashe Suleiman, mai biyayya ga kasurgumin dan bindigan da aka kashe a baya wato Halilu Sububu, a lokacin da yake yunkurin kai wa Turji dauki a Dajin Fakai.

Rundunar ta bayyana wannan nasarar da suka samu a matsayin wani gagarumin koma-baya ga ayyukan ‘yan bindigan, ganin yadda suke da hannu wajen yin garkuwa da mutane da dama a kananan hukumomin Zurmi, Shinkafi, Isa, da Sabon Birni.

-Abdulrazak Bello Kaura

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG