Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Janaral Babangida Ya Kira A Binciki Batun Yin Anfani da 'Yan Mata Suna Kai Kunar Bakin Wake


Janar Ibrahim Babangida.
Janar Ibrahim Babangida.

Tsohon shugaban kasar Najeriya Janaral Ibrahim Badamasi Babangida ko IBB a takaice yace batun yin anfani da 'yan mata suna kai kunar bakin wake abun tayar da hankali ne matuka.

Janaral Babangida yayi magana ne da manema labarai yayin taron addu'oi da aka shirya masa saboda cikarsa shekaru saba'in da uku a duniya. Lamarin yin anfani da 'yan mata suna yin kunar bakin wake abu ne da yakamata a yi bincike mai zurfi akai.

Janaral Babangida yace shawarar da zai bayar ita ce tilas a binciki lamarin a ga yadda har kasar ta kaiga wannan matsayin inda ana anfani da 'yan mata wurin kai kunar bakin wake. Idan aka samu dalilin to za'a san yadda za'a shawo kan lamarin.

Da yake magana akan 'yan matan Chibok da aka sace Janaran yace kamata yayi 'yan kasa su baiwa gwamnati goyon baya domin samun nasarar ceto 'yan matan. A kan ko duniya tana ganin batun 'yan matan ba gaskiya ba ne sai yace ai duniya ta karba kuma 'yan Najeriya sun karba. Magana ce da ta shafi Najeriya gaba daya.

Game da cewa mutanen Najeriya na ganin sojojin Najeriya sun kasa tunda har yanzu basu iya kwubuto 'yan matan Chibok ba sai yace sojoji basu kasa ba. Yayi misali da yakin basasa da kasar tayi. Lokacin da aka soma yakin gwamnati tayi alwashin cewa zata murkushe borin cikin wata daya amma sai da aka yi fiye da shekaru uku ana yaki. Amma a wannan lamarin Janaral IBB yace yayi imani ba za'a kai shekara uku ba kafin a warware matsalar.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG