Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tabbatar Da Mutuwar Mutane Goma Sha Tara A Wata Babbar Girgizar Kasa A Chana


An tabbatar da mutuwar mutane goma sha tara a wata babbar girgizar kasa da ta abkawa wani yanki mai tsaunuka cikin lungu a lardin Sichuan na kasar Chana a jiya Talata.

Hukumomin cikin gida sun ce wasu mutane 247 suka jikata a wannan girgizar kasa da ta fi karfi ko idanunta ke wata gunduma mai suna Ngawa, inda makiyayan kabilar Tibet da Juizhaigou suke zaune, inda kuma nan ne ake da wani gandun shakatawa na kasa wanda dubban mutane daga ciki da wajen China suke ziyarta a duk shekara.

Jami’ai sun ce akalla mutane biyar a cikin wadanda suka mutun yan yawon bude ido ne. Kampanin dillancin labaran kasar Xinhua yace wata mace yar Canada da wani matashi dan kasar Faransa suna cikin wadanda suka jikkata. Xinhua yace an kwashe sama da yan yawon bude ido dubu talatin daga Jiuzhaigou.


Shugaban Chana Xi Jinping ya yi kira ga yan kasar kowa ya bada gudunmuwa wurin aikin ceto da taimakawa wadanda suka jikata.


Hukumar Ayyukan Da Suka Shafi karkashin kasa ta nan Amurka ta ce karfin wannan girgzair ya kai awu 6 da rabi, yayin da takwararta ta kasar China ta ce girgizar ta kai awu 7. Sama da gidaje dubu dari ne suka rushe kuma an dauke wutar lantarki a yankin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG